4 Faburairu 2021 - 12:58
Kotun ICJ, Ta Ce Ta Na Da Halacin Yin Shari’a Game Da Karar Iran

Kotun kasa da kasa ta ICJ, ta bayyana cewa ta na da halacin gudanar da shari’a game da karar Amurka da Iran, ta shigar gaban ta kan takunkuman da tsohuwar gwamnatin Donald Trump ta kakaba mata a shekarar 2018.

ABNA24 : Wannan dai na nufin kotun ta yi fatali da ikirarin Amurka na cewa ba ta halacin gudanar da irin wannan shari’a.

Tuni dai Iran, ta yi maraba da matakin kotun wanda na wucin gadi ne, tana mai danganta hakan da wata babbar nasara a gare ta, game da takunkuman zalincin da Amurka ta kakaba mata, kamar yadda Ministan harkokin wajen kasar, Muhammad Jawwad Zarif, ya wallafa a shafinsa na twitter.

A shekarar 2018 ne Trump ya kakabawa Iran jerin takunkumai na karya tattalin arziki bayan janye kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasasshen duniya suka cimma da Iran din a shekarar 2015.

342/